Ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Ondo ya sauya sheƙa daga PDP ya zuwa APC


Mayowa Akinfolarin, wakili a majalisar wakilai ta tarayya ya sauya sheƙa daga jam’iyar PDP  ya zuwa jam’iyar APC mai rinjaye a majalisar.

Sauya shekar Akinfolarin wanda ke wakiltar mazabar Ileoluji-Okeibo/ Odigbo  dake jihar Ondo an sanar da ita yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A wata wasika da kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya karantawa ƴan majalisar,  ya bayyana rikicin shugabancin jam’iyar PDP a matsayin hujjarsa ta sauya sheƙar.

Sai dai sauya shekar tasa bata gamu da turciya da kuma adawa ba  daga ƴaƴan jam’iyar PDP dake majalisar kamar yadda suka saba nunawa  a baya duk lokacin da aka samu wani wakili a majalisar na shirin barin jam’iyar.

Sauya shekar tasa na zuwa ne watanni biyu bayan da wasu wakilai biyu ƴaƴan jam’iyar ta  PDP suka sauya sheka ya zuwa APC.

Akinfolarin shi ne wakili na 8 a majalisar dake barin  PDP a cikin shekara guda kuma dukkaninsu sun bayyana rikicin shugabanci a matsayin hujjarsu ta sauya sheƙar.

You may also like