Ɗan shekara 36 yayi wata yarinya ƴar shekara 6 fyaɗe a Ibadan


Child_Rape

An gurfanar da wani mutum mai suna Chinaza Azuibuik ɗan shekara 36 a gaban babbar kotun jiha ta jihar Oyo dake Ibadan bisa zargin yiwa wata yarinya mai shekara 6 fyaɗe.

Mai gabatar da ƙara Mista Abdulrazak Alimi ya faɗawa kotun cewa mutumin da ake zargi ya saɓawa shari’a inda ya sadu da yarinyar batare da amincewarta ba.

Yace mutumin ya aikata mummunan aikin ne a ranar 4 ga wata Afirilu na shekarar 2015 a unguwar Oke Adu dake garin Ibadan.

Laifin ya saɓa da shafi na 357,38 cikin baka mujalladi na 11 na kundin dokar manyan laifuka ta jihar Oyo.

Wanda ake ƙara ya musalta dukkanin zargin da ake masa.

Da yake bada shaida a gaban kotun,shaidar mai gabatar da ƙara Sajan Eghune Emmanuel yace mahaifiyar yarinyar Misis Victoria Augustine ta shigar da ƙara a caji ofis na ƴansanda dake Mapo.

Yace an bawa Misis Agustine takardar binciken lafiya inda takai asibitin Adeoyo  domin duba lafiyar ƴarta

“Lokacin da ta dawo da takardar bincken likita daga asibitin Adeoyo binciken ya nuna lallai anyi lalata da ƴarta”yace

Mai gabatar da ƙara ya nemi da a ɗaga shari’ar domin bashi dama ya gabatar cikakkun takardu a gaban kotun

Lauyan wanda ake ƙara Mista Kelvin Akinoye baiyi tirjiya ba kan batun neman ɗaga shariar da mai gabatar da ƙara yayi.

You may also like