Ƙarancin mai: Atiku ya jajantawa yan Najeriya


Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar kan ƙarancin mai da ake fuskanta.

Mokonni uku da suka gabata kenan yan Najeriya na fuskantar wahalhalu a gidajen mai.

Wasu masu  motocin ma sukan kwana a kan layin mai kafin su sayi mai a farashin da gwamnatin ta yarda a sayar.

Atiku ya mika sakon jajen ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Ina mika sakon alhinina  ga kowa da kowa dake kokarin ganin abokansu, da iyalansu a wannan lokaci na farin ciki  saboda karancin mai kuma ina da yaƙinin cewa idan muka hada kan mu a matsayin ƙasa zamu iya nemo mafita daga wannan hali da muke ciki.” Ya ce 

You may also like