Ƙarancin Mai: Buhari ya godewa yan Najeriya kan hakurin da suke yi 


A karon farko cikin makonni biyu shugaban kasa Muhammad Buhari yayi magana da yan Najeriya kai tsaye kan wahalar karancin mai da ake fuskanta a kasarnan.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan lamarin, shugaban ƙasar ya godewa yan Najeriya  kan irin hukurin da suke yi.

Ya ce ya samu tabbaci daga kamfanin mai na kasa NNPC cewa matsalar za ta kau nan ba da dadewa ba.

Shugaban ya bayyana hakane cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi.

“Karancin mai da ake fuskanta a fadin ƙasarnan abin takaici ne,Ina tausayawa dukkanin yan Najeriya kan yadda suke jure bin layukan gidajen mai,”sanarwar tace.

“An sanar dani bayanai akai-akai, musamman kan yadda NNPC ke ƙoƙarin ganin mai ya wadata a wannan lokaci dama nan gaba baki daya.

“Na samu tabbaci daga NNPC cewa za a samu wadatuwar man nan da yan kwanaki kaɗan yayin da ake samun jiragen ruwa dauke da man na isowa kuma ana rarraba shi ko ina cikin kasarnan.

“Bari na kara tabbatar da cewa hukumomin da abin ya shafa za su ci-gaba da fitar da bayanai akai-akai kan halin da ake ciki.Nagode da hakurin da kukeyi  da kuma fahimta.”

You may also like