Ƙarancin Mai: Kamfanin NNPC ya tura tankokin mai 250 zuwa Lagos


Kamfanin Mai na Kasa NNPC, ya ce ya tura tankokin mai 250 zuwa birnin Lagos domin shawo matsalar karancin mai a birnin.

Ndu Ughamadu, mai magana da yawun kamfanin shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

Ya ce an samu sauyi kaɗan kan yadda ake raba mai a birnin Lagos inda a yanzu manyan dillalan mai ne ke samarwa da birnin mai.

“A karshen mako an samu matsala wajen sauke mai daga jirgin dakon ɗaukar mai,wacce tuni aka shawo kanta, yau motoci 250 aka tura cikin Lagos idan aka kwatanta da  kasa da 200 da aka saba turawa birnin a ƙarshen mako.” Ya ce.

Ughamadu ya shawarci masu motoci da su guji boyewa ko kuma sayan man da yawa saboda fargabar fuskantar karancinsa anan gaba inda yace akwai isasshen mai a ajiye da zai dauki kwanaki bai ƙare ba.

You may also like