Ƙungiyar Dillalan Motoci Ta Jihar Kaduna Ta Nesanta Kanta Daga Zargin Ƙona Motar Hukumar Kwastan Ƙungiyar  Dillalan Motoci ta Jihar Kaduna ta nesantar da kanta dangane da Ƙona  wata Motar hukumar Kwastan da wasu bata gari sukayi a Kaduna ranar Alhamis din data gabata. 

Lokacin da yake jawabi a yayin wani ganawa da manema labarai da Kungiyar tayi a Kaduna, Jami’in yada labarai na hukumar Alhaji Muhammad Attahiru White White, yace ko kadan ba ‘ya’yan Ƙungiyar su bane sukayi wannan ta’asa, domin a fili yake ‘ya’yan Kungiyar Dillalan Motoci ta Jihar Kaduna mutane masu sanin ya kamata da kuma da’a, kuma sannan da akwai kyakkyawar alaka da fahimta a tsakaninsu da hukumar Kwastan, wanda babu dalilin da zai sanya su aiwatar da wani abu makamancin haka. 

Ƙungiyar  Dillalan Motocin sun kuma yi kira ga jama’a baki daya da cewar su kasance masu bin doka da Oda gami da martaba hukumomin gwamnati su guji daukar doka a hannun su, sannan sun tabbatar da cewar su mutane ne masu neman arziki ba masu neman tashin hankali ba, babu dalilin da zai sanya su kona dukiyar wani, ballantana dukiyar hukuma, ya kamata mutane su gane haka.

You may also like