Ƙungiyar Kwadago Za Ta Yi Waje Rod Da Gwamnonin Da Suka Ƙi Biyan Albashi A 2019


Shugaban Kungiyar Kwadago, Kwamred Ayuba Wabba ya nemi ma’aikatan gwamnati sun tabbatar su da iyalansu sun mallaki katin zabe don ganin sun yi waje Rod da gwamnonin da ba su biyan hakkokin ma’aikata.

Ya ce, abin bakin ciki ne kan yadda wasu Gwamnoni ke kin biyan albashi da alawus alawus na ma’aikatan jihohinsu da gangan inda ya nuna cewa rashawa ta yi katutu a mafi yawan jihohin.

You may also like