Ƙungiyar Rigar Ƴanci Ta Kai Ziyara Fadar Sarkin Anka


Shahararriyar Kungiyar nan mai rajin Kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta Kai ziyarar aiki ga fadar mai martaba sarkin Anka, Alh. Dr. Attahiru Muhammad kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Zamfara.

Shugaban Kungiyar na kasa da kasa kwamared mustapha Haruna Khalifa shine ya bayyana mana haka a yayin tattaunawar sa da manema labarai, inda ya ce wajibi ne Al’umma su maida hankalin su wurin sarakuna domin jin bukatocin mabukata, sarakuna sune suka fi kusanci da Al’umma.

Ya kara da cewa wannan tattaunawar tamu da mai martaba ta Bada cikakken dama kuma da yardar Allah zamu rage yawan zawarawa da fatara a tsakanin al’uma musamman mata domin samarwa mace daya mafita dai dai yake da raya Al’umma.

Kazalika ya bayyana cewa, da zaran sun kammala shirye- shiryensu, za su sanar da Al’umma na aurar da zawarawa Dari biyu.

Daga karshe Shugaban kungiyar ya yaba da irin goyon baya da suka samu daga Sarkin anka, inda ya kammala da yi wa Zamfarawa fatan alkhairi.

You may also like