Ƙuri’unku Ne Zasu Kawo Canji A Najeriya – INEC


Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, Farfesa Yakubu Mohammed ya tabbatarwa ‘yan Nijeriya da cewa kuri’unsu ne kadai zai tabbatar da wadanda za su shugabanci kasar nan a 2019.

Ya ce, hukumar INEC tana hasashen kimanin ‘yan Nijeriya milyan 85 ne za su samun yin rajistar kada kuri’a a zaben 2019 wanda a cewarsa, wannan adadi shi ne na biyu wajen yawa a duniya bayan Amurka.

You may also like