‘Ƙararraki kan zaɓen shugaban ƙasa ba za su hana miƙa mulki ga Tinubu ba’



Shugaba Buhari da sakataren gwamnatin tarayya

Asalin hoton, Fadar shugaban ƙasa

Bayanan hoto,

Gwamnatin tarayyar ta ce ta kammala shiri don ganin an miƙa muki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga wata Mayun 2023

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa duk da kalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da wasu jam’iyyu ke yi ba zai hana ta miƙa wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu mulki ba.

Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, ya ce sun shirya tsaf domin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba.

Mustapha ya ce ƙarar da wasu jam’iyyu suka shigar kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da jam’iyyar APC da kuma INEC ba zai dakatar da shirye-shiryen da suke yi ba.

Ya ce tuni shirye-shiryen kwamitin ya yi nisa, inda ya ce an ɗora wa ƙaramin kwamitin tsaro na miƙa mulkin da ya tabbatar da cewa babu wani mahaluki da zai kawo tarnaki ga shirin miƙa mulkin.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like