
Asalin hoton, Getty Images
Sai dai kuma Chelsean na son sayo Gavi ta rika ba shi albashi mai yawa
Watakila Chelsea ta sayar da manyan ‘yan wasanta kusan tara saboda karancin kudi inda ake ganin Christian Pulisic, ya kasance daya daga cikin wadanda za su bar kungiyar. (Mirror)
Amma kuma kungiyar na shirin zawarcin matashin dan wasan Barcelona Gavi da albashin da zai sa dan Sifaniyar mai shekara 18 zama cikin wadanda aka fi biya a gasar Premier. (AS )
Dan wasan tsakiya na Brighton Alexis Mac Allister na tawagar Argentina mai shekara 24 ya zama wanda Liverpool ta fi son ta saya a bazara mai zuwa. (Football Insider)
Shi kuwa Wilfried Zaha, dan Ivory Coast zai yi watsi da bukatarsa da wata kungiya a Saudiyya ke yi inda yake son ci gaba da wasa a Turai idan kwantiraginsa ya kare da Crystal Palace a karshen kakar nan. (Evening Standard)
Harry Kane, zai tsaya ya yi nazari sosai a kan sabon kwantiragi da kungiyarsa Tottenham za ta gabatar masa da zarar ta nada sabon kociya , yayin da Manchester United da Bayern Munich ke sha’awarsa. (90min)
Manchester City da Liverpool na harin matashin dan bayan Chelsea Levi Colwill, mai shekara 20 wanda yanzu yake zaman aro a Brighton. (Standard)
Bayan Colwill, Liverpool na kuma sha’awar dan wasan tsakiya na Chelsea din Conor Gallagher, na Ingila da kuma Mason Mount. (Football Insider)
To amma kuma ana sa ran Chelsea za ta yi kokarin shawo kan Mount ya sabunta kwantiraginsa. (ESPN)
Kungiyar ta Stamford Bridge ta kuma tattauna da kociyan Sporting Lisbon Ruben Amorim, mai shekara 38, a fafutukar da take yi ta neman sabon mai horad da ‘yan wasanta na dindindin. (Guardian)
Haka kuma The Blues din na da kwarin gwiwa cewa za su yi nasarar sayen
dan gaban Najeriya na Napoli Victor Osimhen, ko da kuwa ba su samu gurbin gasar Zakarun Turai ba a kaka mai zuwa. (90min)
Manchester City na cikin kungiyoyin da ke sa ido a kan matashin dan bayan Portsmouth Koby Mottoh dan Ingila mai shekara 16. (Football Insider)
Barcelona ta kusa cimma yarjejeniyar daukan kyaftin din Manchester City Ilkay Gundogan, dan Jamus. (90min)
Liverpool na cikin kungiyoyin da ke bibiyar dan gaba na gefe na Lyon Bradley Barcola, na tawagar Faransa ta ‘yan kasa da shekara 21. (Fabrizio Romano)
Roma na sha’awar daukan Roberto Firmino idan kwantiraginsa ya kare da Liverpool a bazaran nan. (Nicolo Schira)
Haka kuma Romar na duba yuwuwar daukan aron dan bayan Leicester City da Ingila James Justin, tare da zabin rike shi gaba daya a kan yuro miliyan 20. (Calciomercato)
Fulham za ta sanya farashin fam miliyan 60 a kan dan wasanta na tsakiya Joao Palhinha mai shekara 27, dan Portugal, wanda Manchester United ke so. (Metro)