Ƙungiyar JOHESU ta janye yajin aikin da take yi


Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiya,ta JOHESU ta dakatar da yajin aikin da yayanta suka shafe kwanaki 44 suna yi.

Kungiyar ta umarci dukkanin yayanta da su koma bakin aiki ranar Litinin 4 ga watan Yuni.

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da aka fitar a karshen taron shugabannin kungiyar JOHESU na kasa da kuma na kungiyar kwararru dake aiki a fannin lafiya da ake kira AHPA.

Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan da ta gabatarwa da kwamitin zartarwata rahoton nasarorin da aka samu a ganawar da suka yi da shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Bayan doguwar tattaunawa majalisar zartarwar kungiyar ta amince da janye yajin aikin domin tausaya yan Najeriya kan mawuyacin halin da suka shiga.

Mambobin kungiyar ta JOHESU sun tsunduma yajin aiki ne a ranar 18 ga watan Afirilu.

You may also like