
Asalin hoton, Getty Images
A watannin baya ne mata da sauran ɗalibai a Jami’ar Kabul suka sake komawa karatu bayan Taliban ta ƙwace iko
Ƙungiyar Taliban ta sanar da hana mata zuwa jami’o’i a ƙasar Afghanistan, a cewar wata wasiƙa daga ministan ilmi mai zurfi.
Ministan ya ce wannan mataki zai ci gaba har zuwa lokacin da za a ji sanarwa ta gaba. Ana sa ran wannan mataki zai fara aiki ne nan take.
Sanarwar ta kuma taƙaita wa mata hanyoyin samun ƙa’idajjen ilmi, don kuwa tun tuni Taliban ta ware mata daga halartar mafi yawan makarantun Sakandire.
Wata ɗalibar Jami’ar Kabul ta faɗa wa BBC cewa tun bayan jin wannan labari take ta sharɓar kuka.
Wata ukun da ya wuce ne dubban mata da ‘yan mata a faɗin Afghanistan ne suka zauna suka rubuta jarrabawar shiga jami’a.
Sai dai an taƙaita wa matan gaba ɗaya darussan da za su iya karanta, inda aka hana su karanta fannin kimiyyar likitanci dabbobi da injiniyanci da nazarin tattalin arziƙi da noma, sannan kwata-kwata ba za su karanci aikin jarida ba.
Bayan ƙungiyar ta ƙwaci mulki bara, jami’o’i suka ɓullo da tsarin azuzuwa masu raba tsakanin maza da mata, haka ma ƙofofin shiga duk an bambanta.
Haka zalika, ɗalibai mata, malamai mata ne kawai ko tsofaffi za su iya karantar da su.
‘Sun rusa gadar rayuwata’
Da take mai da jawabi game da wannan haramci na baya-bayan nan, wata ɗalibar jami’a ta faɗa wa BBC cewa tana tunanin ƙungiyar Taliban na tsoron mata ne da kuma irin ƙarfin ikon da suke da shi kawai.
“Sun ruguza gadar da kawai za ta iya haɗa ni da kyakkyawar makomar rayuwata,” in ji ta.”To, ya zan yi? Na yi imanin cewa zan iya karatu, na canza rayuwata ko na haskaka rayuwata amma sun ruguza wannan lissafin.”
Sashen ilmi na Afghanistan ya samu gagarumar illa, tun bayan karɓe ikon da Taliban ta yi, kuma an samu kwararar masu ilmi da suka ƙware zuwa ƙasashen waje jim kaɗan da janyewar dakarun da Amurka ta mara wa baya a bara.
Wata mata ta yi bayani game da “wahalhalu masu yawa” a ƙoƙarinta kawai na ci gaba da neman ilmi bayan ƙwace mulki da Taliban ta yi.
Ta faɗa wa BBC: “Mun yi faɗa da ‘yan uwanmu, mun yi faɗa da iyayenmu, mun yi faɗa da al’umma, kai har da gwamnati.”Mun shiga matsanancin hali duk don mu iya ci gaba da karatunmu.”A wancan lokacin aƙalla na cika da farin ciki ko ba komai zan kammala jami’a na cimma burina. Amma, yanzu ta yaya zan rarrashi zuciyata?”
Tattalin arziƙin Afghanistan akasari ya dogara ne kan tallafin da ƙasar ke samu daga ƙetare a ‘yan shekarun nan, ƙungiyoyin ba da agaji a wani ɓangare sun janye, a wasu sassa ma gaba ɗaya sun janye taimakon da suke bai wa ɓangaren ilmi tun lokacin da Taliban ta ƙi amincewa ta bar ‘yan mata su je makarantun sakandire.
Malaman da ke koyarwa da suka rage a ƙasar kan kwashe tsawon watanni ba tare da an biya su albashi ba.
Matakan na baya-bayan nan mai yiwuwa za su ƙara janyo damuwa a tsakanin ƙasashen duniya.
Amurka da sauran ƙasashen Yamma sun gindaye sharaɗin bunƙasa ilmin ‘ya’ya mata a Afghanistan kafin su martaba gwamnatin Taliban a hukumance.
Mataimakin jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Robert Wood ya yi tur da waɗannan matakai da Taliban ta ɓullo da su a baya-bayan nan.
“Ƙungiyar Taliban ba za ta sa ran zama halartacciyar wakiliya a tsakanin ƙasashen duniya ba, har sai sun mutunta ‘yancin duk wani ɗan Afghanistan,” ya ce.”Musamman ‘yancin bil’adama da ‘yancin tushe na mata da ‘yan mata.”A watan Nuwamba ne, hukumomi suka haramta wa mata zuwa dandalin shaƙatawa a birnin Kabul, suna iƙirarin cewa ba a biyayya ga dokokin addinin Musulunci a can.