Wasu ƴan jam’iya da kuma magoya bayan jam’iyar APC sun sauya sheka ya zuwa jam’iyar PDP a jihar Benue.
Mambobin da suka yi bikin murnar sauya shekar tasu a Otukpa, hedikwatar karamar hukumar Ogbadibo dake jihar sun ce suna ficewa ne daga APC saboda riƙon sakainar kashin da gwamnatin tarayya ke yiwa kisan mutanen da akeyi a jihar a rikici tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma a jihar.
Tuni masu fashin baƙi suka hango cewar akwai yiyuwar mutane da dama za su juyawa jam’iyar APC baya ciki har da gwamnan jihar Samuel Ortom.
Tun da farin gwamnonin PDP biyu Ayo Fayose na jihar Ekiti da kuma Nyesom Wike na jihar Rivers sun ziyarci jihar a kwanakin btdomin jajantawa gwamnan da ma mutanen jihar kan mutanen da suka mutu a rikicin.
Har ila yau gwamnonin sun bayar da gudummawar kudi a wani abu da mutane ke gani sun yi ne domin su ja hankalin gwamnan ya dawo cikin PDP.
Da alama hakan na gwamnonin zai cimma ruwa domin ko da a makon da ya gabata sai da Ortom ya sasanta da mutumin da ya gada akan mulki Gabiel Suswam bayan sun shafe shekara uku basa ga ma ciji da juna.
Da yake magana a madadin masu sauya shekar, Ben Ejibe,tsohon dan takarar majalisar jiha a karkashin jam’iyyar,ya ce mutane sun yanke shawarar sauya sheƙa zuwa jam’iyar PDP domin su tallafawa jam’iyar a zabe mai zuwa don kawo ƙarshen kisan da makiyaya ke yiwa mata da ƙananan yara.