Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ƴan kwangila a jihar Bayelsa


Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wane ba sun yi garkuwa da wasu ƴan kwangila dake aiki a ɗaya daga cikin aiyukan hukumar raya yankin Niger Delta (NNDC) a ƙaramar hukumar Ogbia dake jihar Bayelsa.

Asinim Butswat, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ‘yan sanda sun kama wani dake da hannu a lamarin ana kuma cigaba da yi masa tambayoyi.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya ruwaito Lucky Moses daya daga cikin sshugabannin al’umma a yankin na cewa ƴan bindigar sun dirarwa ƙauyen   da safiyar ranar Talata.

“Ƴan bindigar sun zo inda suka shiga musayar wuta da sojoji kafin su ɗauke mutanen da suke fako,” Moses yace.

“Mutanen da  aka sace su biyu ne  amma an saki daya nan take ya yin da aka yi awon gaba da ɗaya a cikin jirgin ruwa mai gudun gaske.”

You may also like