Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci A Jihar Neja Masu garkuwa da mutane wadanda zuwa yanzu ba a kai ga gane su ba, sun yi garkuwa da Alkali Abubakar Jibrin na kotun shari’ar musulunci a kauyen Jermiya dake karamar hukumar Rafi a Jihar Neja.

Majiyar mu ta ruwaito cewar masu garkuwa da mutanen su 18 suka farwa kauyen dauke da muggan makamai, inda suka yi garkuwa da Alkalin a hanyar sa ta dawowa daga aiki kilomita goma kafin shiga garin Pandogari da misalin karfe shida na yamma.

Al’amarin ya faru ne kwanaki uku da sace mutane bakwai, inda masu garkuwa da mutanen suka kashe mutum uku a hanyar Alawa zuwa Pandogari.

Hakimin garin na Alawa Ibrahim Saleh ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya kara da cewar “masu garkuwa da mutanen sun bukaci a ba su kudin fansa kimanin naira miliyan hamsin kafin su sako Alkalin.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya baiyana cewar suna iya kokarin su wurin ganin sun kubutar da alkalin cikin koshin lafiya.

You may also like