Ƴan fashi sun liƙe bakin tsohuwa mai shekaru 89 da sufa gilu


An kama wasu mutane biyu da laifin yiwa wata mata, Imasogbonre Enahoro mai shekaru 89 fashi da makami kana suka like mata baki da sufa gilu.

Enahoro da Marylyn Ajibola ƴarta  wacce itama aka liƙe mata bakin da sufa gilu an yi musu fashin kayayyaki masu muhimmanci ciki har da mota ƙirar Toyota Camry a gidansu dake ƙauyen Igueben kusa da Benin babban birnin jihar Edo.

Mutanen da ake zargi da aikata laifin sun liƙe bakin tsohuwar da kuma yarta saboda kada su kira taimako.

Ajibola,wacce tace lamarin yafaru da misalin karfe 5 na yamma ta iya gane daya daga cikin mutanen da suka aikata laifin a hedikwatar a rundunar yan sandan ta jihar.Tace mai laifin shine ya mari mahaifiyarta.
Daya daga cikin mutanen  da ake zargi da aikata laifin mai suna Kingsley yace motar da suka sata tana nan ba a sayar da ita ba.

“Lokacin da mukaje gidan Mama bata da kuɗin da zata bamu.biyu daga cikin mu sun tsaya daga waje Tosin ya shiga ciki.Mun samu  ₦7200 ne kawai a cikin motar,”yace.

“Bani da masaniyar cewa  an rufe bakin Mama da sufa gilu saboda ban shiga ciki ba najira ne daga waje. Bamu sayar da motar ba,Tosin ne yace zai yi amfani da ita  amma mun fada masa cewa babu ta yadda za ayi mu cigaba da zama da shi a jihar  Osun.

“Bazan iya zama a gidan babansa ba, bana aikin komai motar har yanzu tana jihar Osun.”

Daya daga cikin mutanen da ake zargi har yanzu bai shiga hannun jami’an tsaro ba.

Kwamishinan yan’sandan jihar, Babatunde Kokumo yace nan bada jimawa ba za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

You may also like