Ƴan Jam’iyyar APC Da Dama Sun Canza Sheƙa Zuwa PDP A Jihar Neja



Yayin da ake murnar bikin sabuwar shekara ita kuwa jama’iyyar adawa ta PDP ta kara ne da murnar karbar ‘ya’yan jama’iya mai mulki ta APC sama da dubu daya da suka canja sheka zuwa jama’iyar adawa ta PDP a karamar hukumar Mashegu daya daga cikin kananan hukumomin shiyyar Neja ta Arewa inda gwamnan Jihar ya fito.

Taron karbar ‘ya’yan jama’iyar ta APC da ya gudana a shekaran jiya talata a filin taro na makarantar sakandaren jeka kadawo dake garin Saho-Rami wanda yasamu halartar masu sauya shekar daga ilahirin gundumomin karamar hukumar ta Mashegu da manyan jigogin jama’iyar adawa ta PDP a Jihar ta Neja

Sauya shekar na ranar Talata shine karo na biyu a yankin Neja ta Arewa a cikin watanni uku, inda ko a ranar 04/11/2017 daruruwan ‘ya’yan jama’iyar APC suka sauya sheka zuwa jama’iyar adawa ta PDP a garin Kontagora mahaifar gwamnan Jihar ta Neja Alhaji Abubakar Sani Bello.

Da suke karbar ‘ya’yan jama’iyar ta APC da suka sauya shekar, tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Neja Rt. Honorabul Muhammad Muhammad Alkali da tsohon kwamishinan harkokin addini a zamanin gwamnatin PDP na Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna) Alhaji Shehu Haruna Kumbashi sun baiyana cewar sauya shekar na ‘ya’yan jama’iyar APC alamune karara dake nuna kasawar gwamnatin APC inda ta kasa cika dinbin alkawarurrukan da suka daukarwa al’umma.

Sun kara da cewar jama’iyar PDP zata tafi da kowa a matsayin uwa daya uba daya batare da nuna banbanci ko wariya ba, mun koyi darussa a kura-kuran da mukayi a baya, yanzu mun shirya tsaf domin karbe mulki a hannun gwamnatin APC mai alkawari ba cikawa-Inji su.

Da yake jawabi a madadin ‘ya’yan jama’iyar APCn da suka sauya shekar Mallam Munir Muhammad ya ce ” mun yanke shawarar komawa jama’iyar PDPn ne saboda gwamna Abubakar Sani Bello ya kasa cika alkawarurrukan da ya daukar mana na samar mana da abubuwan more rayuwa da jindadin alumma a karamar hukumar mu wanda sune babban kalubalan da muke fama dashi.

Muhammad ya kara da cewar ” ba wani tartibin cigaba da zamu gani kasa da shekara daya da ‘yan watanni da suka ragewa gwamnan a karagar mulki duba da ba wani tanadi da gwamnan yayi muna na gyaran dinbin hanyoyin mu da suka lalace da sanya wutan lantarki a mafi akasarin garuruwan dake karamar hukumar mu a cikin kasafin kudin shekarar 2018.

A kwai ta kaici irin yadda gwamnatin jama’iyar APC sukayi mana alkawarurrukan magance muna dinbin matsalolin ababen more rayuwa da jindadin al’umma da muke fama dashi a lokacin yakin neman zabe wanda hakan yasa muka bada cikakken goyon bayan mu tare da jajircewa dan ganin ankai ga nasara duba da gwamnan ya fito daga wannan yanki namu na Zone C munyi tsammanin zamuga ribibin ruwan aiyukan raya kasa kamar yadda muke gani a wasu jihohin, amma a yanzu anyi watsi damu ba wani sahihin cigaba da muka gani gwarama mulkin PDP da wannan, hakan yasa muka yanke shawarar komawa jama’iyar ta PDP.

A nasa jawabin yayin taron, shugaban jama’iyyar PDP na karamar hukumar Mashegu Mallam Sani Musa ya baiyana cewar ” sauye-sauyen shekar da ake cigaba da samu daga jama’iyar APC mai mulki zuwa PDP alamune da ke nuna jama’iyar PDP ta shirya tsaf domin karbe mulki a hannun jama’iyar APC wanda ta rasa a shekarar 2015.

You may also like