Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya bayyana cewa ‘yan majalisar tarayya ne za su fi kowa kokawa kan matakin da suka dauka na canja ranar zaben Shugaban kasa ta yadda suka rabe ranakun zabensu da na Shugaban kasar.
Gwamnan ya jaddada cewa mafi yawan ‘yan majalisar sun dogara ne da farin jinin Shugaba Buhari wajen lashe zaben inda ya nuna cewa a bisa wannan sabon tsarin na fara zaben majalisar tarayya, mafi yawansu za su rasa kujerarsu.