Rundunar Sojan Nijeriya ta musanta zargin gwamnatin Yobe kan cewa sakacinsu ne ya janyo mayakan Boko Haram suka samu nasarar arcewa da ‘yan Matan Sakandaren Dapchi na jihar a ranar Litinin.
Kakakin Rundunar, Birgediya Janar Jude Chukwu ya ce an girke sojoji a wani wuri mai nisan kilomita 30 daga makarantar kafin harin. Tuni dai, wasu suka yi Allah wadai kan wannan cacar bakin a daidai lokacin da ya dace bangarorin biyu suka hada kai don ganin an ceto ‘yan Matan.