Ƴan Matan Dapchi: Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Jihar Yobe


Yanzu-yanzun nan tawagar Gwamnatin Tarayya ta isa Birnin Damaturu, Fadar Jihar Yobe, don ganawa da Jami’an Gwamnatin Jihar, Shugaba makarantar yan mata na Dapchi wanda aka sace dalibanta, Jami’an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki na jihar, don sanin halin da ake ciki a fafutukar ceto ‘yan matan.

Tawagar ta haɗa da ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, Ministan harkokin cikin gida Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) da sauransu.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin kwanaki huɗu da tawagar gwamnatin tarayya ke ziyartar jihar Yobe tun bayan ba tar ƴan matan Dapchi.

You may also like