Ƴan Najeriya Ne Zasu Bada Shaida Kan Buhari Ba Obasonjo Da IBB Ba – Bola Tinubu


Tsohon Gwamnan Legas kuma jigo a APC, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ‘yan Nijeriya ne kadai za su yanke hukunci kan makomar gwamnatin Shugaba Buhari amma ba tsoffin shugabannin kasar nan ba.

Tinubu ya nemi Cif Olusegun Obasonjo da Ibrahim Badamasi Babangida kan su kyale Buhari ya ci gaba da tafiyar da harkokin mulkinsa a maimakon yadda suke nuna masa adawa karara.

You may also like