Ƴan sanda huɗu sun ɓace bayan ƴan bindiga sun buɗewa motarsu wuta a jihar Benue


Ƴan sanda huɗu dake aiki da rundunar ƴan sanda ta jihar Benue aka tabbatar sun yi ɓatan dabo bayan wani hari da ake kyautata fulani makiyaya ne suka kan jerin gwanon motocin da suke ciki a yayin da suke sintiri ranar Asabar a jihar.

Moses Yamu mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar harin.

Maharan sun yi wa jami’an ƴan sandan ruwan wuta  akan hanyarsu ta dawowa daga aikin samar da tsaro a wasu ƙauyuka dake ƙaramar hukumar Logo ta jihar.

Maharan sun kuma samu nasarar ƙona motar da jami’an ƴan sandan ke ciki ya yin harin da yafaru da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Wata sanarwa daga Yamu ta ƙara da cewa ba a iya tantance yawan mutanen da suka jikkata a ɓangaren maharan waɗanda ke dauke da muggan makamai.

Yamu ya ƙara da cewa rundunar na na ƙoƙarin gano ƴan sanda ukun da huɗu da suka ɓace.

You may also like