Ƴan Sanda Sun Dawo Da Kuɗaɗe Da Takardun Bayanan Kasafin Kuɗi Da Suka Ƙwace A Gidan Sanata Danjuma Goje


goje

Ƴan sanda sun dawo da kuɗi na gida da kuma ƙasashen waje haɗi da wasu muhimman takardu da sukayi awon gaba dasu a kwanakin baya daga gidan tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanata a yanzu, Danjuma Goje.

Wata majiya dake kusa da tsohon gwamnan tace ƴan sandan sun dawo da kuɗaɗen da kuma muhimman takardu bayan kasafin kuɗin shekarar  2017 bayan da suka gano cewa bayanan da suka samu daga wani mai kwarmata bayani bana gaskiya bane.

“ƴan sandan Najeriya yau da safen nan, sun dawo da dukkanin abubuwan  da suka ɗauka daga gidan Sanata Goje, da suka haɗa da kuɗi da kuma wasu takardu dake da alaƙa da kasafin kuɗin wannan shekarar dake gaban majalisa.Inda suka ce an samu kuskuren a bayanan da suka samu daga wani mai kwarmata bayanai”

Idan dai za’a iya tunawa a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne ƴan sanda suka kai sumame gidan sanata Goje dake Abuja.

Ko da a jiya Laraba, sai da majalisar ƙasa tace ƴan sanda sun ɗauki wani bangare cikin takardun kunshin kasafin kudin wannan shekara, a sumamen da suka kai gidan sanatan wanda shine shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar dattijai.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like