Ƴan sanda sun kama mutane biyu da ake zargi sun kashe wata dalibar jami’ar ABU


Ƴan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da hannu a kisan wata dalibar jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya  ranar juma’ar da ta gabata.

Marigayiyar wacce ɗaliba ce dake ajin farko na tsangayar karatun likitan dabbobi wacce aka bayyana da suna Deborah, an rawaito cewa sai da aka yi mata fashin wayoyin hannunta  biyu kafin a kashe ta.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi an kama shi ne ranar Lahadi ɗayan kuma ranar Litinin kuma dukkaninsu suna tsare a hannun jami’an tsaro.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu yace tuni aka gano daya daga cikin wayar hannun ya yin da suke cigaba da neman dayar.

“Mun kama ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi a PZ dake Zariya da waya guda ɗaya bayan yi masa tambayoyi ya kai mu wurin ɗayan amma abin takaici da muka isa wurinsa ya riga ya sayar da wayar hannun ga wani da yake sayan wayoyin hannu,na sata.”

Yace tuni aka fara bincike kan dalilin da yasa suka kashe dalibar bayan sun kwace mata wayoyin hannunta biyu.

You may also like