Ƴan sanda sun kama wani lauyan bogi da ya shafe shekara 15 yana aiki


Bayan da ya shafe shekara 15 yana aiki a matsayin lauyan bogi yanzu dai za a iya cewa ruwa ya karewa dan kada domin kuwa dubin, Lauya Chris Elisha ta cika bayan da shari’a ta kama shi.

Ƴan sanda dake ƙarƙashin caji ofis na Ojo a jihar Lagos sun kama mutumin mai shekaru 49 bayan da wani lauya, Nnamdi Okafor ya  nuna shakku akan ingancin lauyan dake kare wani  mai laifin a gaban kotu.

Jaridar Punch ta gano cewa lauyan ya a gaban kotun a ranar domin ya kare wani mutum da ake zargi da aikata laifin kuma yan’sanda suka gurfanar da shi gaban kotun.

Lauyan na bogi ƙoƙarinsa na neman belin mutumin da yake karewa ne ya karanto wani sashi kundin tsarin mulkin ba dai-dai ba hakan ya jefa shakku a zukatan mutanen dake kotun game da ingancin karatun lauyan.

Hakan ya sa lauya Nwafor wanda shima ya halacci zaman kotun ya tuntubi ya kalubalanci  Elisha bayan kammala zaman kotun, kan cewa shi ba lauyan gaske bane. Hayaniyar da ta kaure a tsakaninsu ya jawo hankalin jami’an ƴan sanda dake harabar kotun zuwa wajen inda suka yi awon gaba da mutumin da ake zargi.

Binciken da ƴan sanda suka gudanar a gidansa sun samu nasarar gano hular lauyoyi da kuma wasu kayayyaki dake da alaƙa da aikin lauya.

You may also like