
Ƴan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar kawar da wani hari kan wasu ƙauyuka biyu dake karamar Hukumar Talatar Mafara bayan da suka shafe awanni suna musayar wuta da gungun wasu ƴan bindiga.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Muhammad Shehu ya shedawa jaridar Daily Trust cewa, yan bindigar da suka kai hari kan ƙauyen Birane dake karamar hukumar Zurmi ƴan makonnin da suka wuce, sune suka shirya kai hari kan ƙauyukan Ruwan Gizo da Yar Tasha a ƙaramar hukumar Talata Mafara amma an samu nasarar fatattakarsu.
“Mun yi musayar wuta da su. mun samu nasara a kansu an kashe ɗaya daga cikinsu yayin da aka samu bindigar Ak-47 guda biyu da kuma baburan hawa da dama daga hannunsu,” ya ce.
Yace ɓatagarin suna kan shirinsu na kai wa kauyukan hari tare da yin garkuwa da mutane. Tuni sun riga sun yi garkuwa da wani mai suna Bilyaminu Abdullahi kafin ƴan sanda su iso ƙauyen.
Ya kara da cewa “An ceto mutumin da aka yi garkuwar da shi yayin da aka harbe daya daga cikin yan bindigar wasu daga cikinsu kuma suka tsere da raunuka harbin bindiga iri-iri kuma ƴan sanda za su kamo su tun an bi sawunsu.”