Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta nanata cewa a shirye take ta samar da cikakken tsaro da zai samar da yanayi mai kyau a lokacin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 17 ga watan Faburairu.
Undie Adie, kwamishinan ƴan sandan jihar shine ya bayar da wannan tabbaci lokacin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar dake Jos.
Adie wanda yake amsa tambaya kan jijitar da ke yawo a gari cewa ba za’a gudanar da zaɓe ba a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa saboda rashin tsaro, ya ce,”Nagode Allah da kace jita-jita.labarin ba gaskiya bane, ƴan sanda a shirye suke su samar da tsaro lokacin zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomi 17 da suke jihar,”
Kwamishinan ya ƙara da cewa matsalar rashin tsaro ta ragu sosai a jihar kuma tuni zaman lafiya ya dawo ko da a wuraren da suka fuskanci rikici a baya.