Ƴan Sanda Sun Tarwatsa Magoya Bayan El Zakzaky A Kaduna 


Rundunar ƴan sandan Kaduna ta yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa gungun magoya bayan Shugaban ƴan Shi’a, Malam Ibrahim El Zakzaky a lokacin da suke gudanar da wani tarzoman lumana na neman gwamnati ta sako Shugaban nasu.

Rahotanni daga jihar sun nuna cewa masu tarzoman sun fara taruwa ne a kan titin Nnamdi Azikwe da ke yammancin birnin inda a lokacin da suka iso marabar shiga unguwar Bakin Ruwa, sun haɗu da fushin hukuma wanda kuma a karshe aka samu nasarar murƙushe masu zanga zangar. Tuni dai ƙungiyar Shi’ar ta yi Allah wadai da matakin da rundunar ‘yan sandan ta dauka a kan maniyantq.

You may also like