Ƴan Sanda Sun Yi Awon Gaba Da Aisha BuhariRundunar ‘yan sandan Najeriya shiyar babban birnin tarayya Abuja, ta cika hannu da wata yar damfara mai shekaru 37, yar damfarar wacce take amfani da sunan mai dakin shugaban kasa Buhari, ta shiga hannu ne a lokacin da take kokarin neman alfarmar kontiraki da sunan matar Buhari.

 Majiyar mu ta shafin Madubi ta rubuto cewar, Aisha Buharin Bogi, ta shiga hannun jami’an tsaron ne a lokacin da take kokarin damfarar Ofishin Fadama lll da sunan matar shugaban kasa Buhari.

You may also like