Ƴan Sanda Sunyi Awon Gaba Da Ɗan Bilki Kwamanda


Rahotanni da DUMI-DUMI da suka shigowa kafar Yaɗa labaran Arewa24news yanzu haka ɗan gani kashe nin shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Dan Bilki Kwamanda na hannun rundunar ‘yansandan jihar Kano sashen binciken manyan masu laifuka (CID).

Wannan kamu ana zargin ya biyo baya ne sakamakon bijirewa umarnin haramta masa magana dla gamayyar gidajen rediyon tarayya da ake zargin Fadar shugaban kasa ta kakaba masa.

Danbilki ya yi hira a wani gidan Radiyo mai zaman kansa a jiya Lahadi, wanda Jami’an tsaro suka kewaye gidan suna dakon sa ya fito su kama shi amma ya ki fitowa har tsawon awa biyu. Tafiyar su ke da wuya ya fice tare da fecewa.

You may also like