Rundunar yansandan jihar Kano ta bayar da rancen baburan hawa guda 500 ga kananun jami’an yansanda domin dai saukaka musu wajen zirga zirga ta zuwa wajen aiki da sauran al’amuran yau da kulum.
Kakakin rundunar yansandan jihar Dsp M Majia Ppro Kano yace wannan yana cikin tsarin babban sufeton yansanda, Ibrahim K Idris na nuna halin dattako da tausayin kananun yansanda, hakan ne yasa aka samar da baburan akan farashi mai rahusa domin bawa yansandan wanda sannu a hankali za a runga cirar kudin daga albashinsu har su kammala biya ba tare da an takura su ba.
Dsp Majia, ya kara da cewa ba’a nan kawai babban sufeton ya tsaya ba, yace za kuma a samar da kananun gidaje masu saukin kudi don bada su rance ga jami’an yansanda musamman wadanda basu mallaki muhallin zama ba.
Babban sufeton yansandan kasar nan wanda ya samu wakilcin, AIG DAN BATURE shine ya jagoranci taron bada rancen baburan ga jami’an nw yansanda bayan yayi jawabi game da makasudin da yasa babban sufeton yasa aka samar da baburan.
Kwamashinan yansandan jihar kano, CP Rabiu Yusuf da shima ya kasance a wajen taron yaja hankalin jami’an yansandan da aka bawa baburan da suyi amfani dasu ta hanyar daya dace akan dalilan da yasa aka basu rancen.