Ƴan Sandan Kano Sun Bada Belin Kwamishinan Da Yace A Jefi Kwankwaso Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gayyaci Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Abdullahi  Abbas, dangane da kalaman haddasa husumar da ya furta, inda ya ce wa magoya bayan Gwamna Ganduje idan Kwankwaso ya shiga Kano da tawagar sa, su yi masa jifar Shaidan.

Abbas, wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, ya furta cewa “Idan Shaidan Kwankwaso ya shigo Kano, ku jefe shi.”

A yanzu dai Kwankwaso na ci gaba da shirye-shiryen sa na shiga Kano tare da babban gangamin da ake sa ran za su haura magoya baya miliyan daya, a ranar 31 Ga Janairu, 2018.

Sai dai kuma Kakakin ’Yan sandan Kano, Magaji Majiya, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an gayyaci Abdullahi Abbas ne tare da wanda ya kai korafin, wato MK Umar, kuma an yi musu tambayoyi dangane da kalaman da su ka furta a kan Sanata Kwankwaso.

Majiya ya kara da cewa, an bada belin Abdullahi Abbas bayan an yi masa tambayoyi, “amma kuma karfin wannan kasassaba da ya yi, ta sa har yanzu ana ci gaba da bincike kan furucin nasa a ofishin binciken masu laifuka, wato CID.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane dangane da wata ba hammata iska da aka yi tsakanin magoya bayan Ganduje da na Kwankwaso, a ranar Lahadi da ta gabata.

Wadanda aka kama din sun hada Sani Abdullahi Abbas, Abbas Abdullahi Abbas da Nazifi Shawiya.

Majiya ya ce da zaran an kammala bincike za a tura su kotu domin a hukunta su.

You may also like