Jami’an ƴansanda huɗu da kuma soja ɗaya sun rasa rayukansu a jihar Lagos


nigeria-police

Fatai Owoseni kwamishinan ƴansanda na jihar Lagos yace rundunar ƴansandar jihar na aiki da sauran takwarorinta na tsaro don ganin ta kama da kuma hukunta ƴan ta’addan da suka kashe jami’an ƴansanda huɗu da kaftin na soja ɗaya da kuma farar hula ɗaya a yankin Ikorodu dake jihar.

Owoseni yayi wannan alƙawarin ne a wata sanarwa da yafitar a ranar lahadi kan harin da yafaru.

Yace jami’an tsaron sun rasa rayukan sune lokacin da suke ƙoƙarin kuɓutar da wasu mutane da akayi garkuwa dasu.

“Da misalin ƙarfe ɗayan daren yau lahadi 9 ga watan Afirilu,ƴansanda sun sami kiran gaggawa cewa wasu gungun ƴan ta’adda/masu garkuwa da mutane sun shiga Owutu-Isowo ta ƙungurmin dajin dake yankin”

“ An samu rahoton cewa sun sace wasu magidanta dake yankin, da samun labarin ƴan sanda da sojoji sun tattara ma’aikatansu don kai ɗauki, kuma akayi nasarar ceto mutanen”

“Amma abin takaici 5 daga cikin jajirtattun ma’aikatan mu sun rasa  rayukansu, guda daga cikinsu Kaftin ne  a rundunar sojin Najeriya, sauran huɗu kuma jami’an ƴansanda ne, ɗaya daga cikin mazauna yankin shima ya rasa ransa”

“Muna addu’ar Allah yasaka musu da gidan Aljanna irin bautar,ya kuma jiƙansu da rahama”

“Muna kuma addu’ar Allah yabawa iyalensu haƙurin jure wannan babban rashin da sukayi “

“Rundunar tana ƙara tabbatarwa jama’a cewa da haɗin kan sauran takwarorinta a harkar tsaro, masu laifin da suke da hannu a wannan mummunan aiki za a kama su,sannan su fuskanci shari’a”yace

You may also like