Ƴansanda sun samu nasarar ceto wasu ƴan ƙasar Afirka ta Kudu da aka yi garkuwa da su a Kaduna


Abba Kyari bayan da suka kammala sumamen

Rundunar babban sifetan ƴansanda ta musamman dake yaƙi da yin garkuwa da mutane sun samu nasarar ceto wasu ƴan ƙasar Afirka ta Kudu da aka yi garkuwa da su a wurin haƙar ma’adanai dake jihar Kaduna.

Kwamandan rundunar ACP Abba Kyari ya shedawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a ranar Asabar cewa an kuma samu kama wasu daga cikin gungun masu garkuwa da mutanen.

Kyari ya ce  Thomas Arnold da Hendrick Gideon an yi garkuwa da su a wurin haƙar ma’adanai dake ƙauyen Maidaro a ranar 23 ga watan Janairu  aka kuma ɗauke su zuwa dajin  Birnin Gwari dake jihar.

Yace an samu nasarar ceto mutanen a ranar Asabar bayan da rundunar ts musamman  ta tsaurara bincike ta hanyar amfani da jirgi mai saukar ungulu da kuma rundunar yan sandan jihar.

“Mutanen an dauke su daga Kaduna zuwa Abuja da safiyar yau inda aka damƙa su ga ofishin jakadancin ƙasar Afirka ta Kudu da kuma wakilan kamfanin da suke wa aiki domin duba lafiyarsu.

“Mutanen da aka ceto suna cikin koshin lafiya kuma suna taimakawa jami’an ƴansanda da bayanai domin su cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.”

You may also like