ƴan bindiga sunyi garkuwa da kwanishina A jihar Cross Rivers


Niger-Delta-Militants-1

Wasu ƴan bindiga sunyi awon gaba da kwamishinan ruwa na jihar Cross River Mista Gabriel Odu-Orji.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa anyi awon gaba da kwamishinan a layin Effionawan dake unguwar Mayne Avenue  dake yankin  Calabar ta kudu.

Wani wanda ya shaida abun da yafaru mai suna James Ibri yace ƴan bindigar su biyar sun biyo Orji lokacin da yake fitowa daga motarsa don shiga gidan cin abinci dake wurin.

\Ibri yace ƴan bindigar sun bar motar da suka zo da ita inda suka umarci kwamishinan da ya shiga motarsa sanfurin Prado inda suka bar wurin batare da ɓata lokaci ba.

“Da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana ina zaune ƙofar shiga wurin cin abincin ina jira abokina, lokacin da kwamishinan ruwa yafito daga motarsa ya nufo wurin cin abincin”Ibri yace

“ kafin yaƙarsa cikin wurin mutane biyar ɗauke da manyan bindigogi suka ajiye motarsu a gefen titi inda suka umarci kwamishinan da yashiga cikin motarsa sannan suka tafi”

Yaƙara da cewa da ganin waɗannan mutanen, masu garkuwa da mutane ne saboda yadda suka rufe fuskokinsu don kar a ganesu.

Mai magana da yawun rundunar ƴansanda ta jihar Irene Ugbo ya tabbatarwa da kamfanin daillacin labarai na ƙasa NAN faruwar al’amarin.

“Mun samu ƙorafi akan an sace kwamishinan ruwa na jiha, anyi garkuwa da shi inda aka tafi dashi motarsa sanfurin  Prado”yace

A yanzu da nake magana mun kafa shingayen binciken ababan hawa a titinan dake birnin don ganin cewa an sako shi.

You may also like