Ƴan Majalissar Sun Shahara Wajen Karɓar Rashawa – Jega


Tsohon Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ( INEC) Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa ‘yan majalisar tarayya sun iya neman cin hanci da rashawa da sunan aikinsu.

Jega ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake gabatar da laccar ranar dimokradiyya inda ya ce, ya tattauna da wasu shugabannin hukumomin gwamnati wadanda suka tabbatar masa yadda ‘yan majalisa ke neman cin hanci daga hannunsu da sunan gudanar da aikin sa ido kamar yadda doka ya tanadar masu

You may also like