Ƴan Shi’ah Za Su Yi Zanga Zangar Da Zata Girgiza Duniya Akan Zakzaky


Kungiyar mabiya addinin Shi’ah sun sanya mako mai zuwa, 15 ga watan Afrilu, a matsayin ranar da zasu yi zanga zangar da zata girgiza duniya don ganin an saki Zakzaky,
haka kuma ita wannan ranar ita ce ta cika kwanaki 100 da fara yin zanga zangar ganin an saki Zakzaky.

A cewar kamfanin dillancin labarai na AhlulBayt, ana sa ran wannan zanga zanga zata mamaye duk duniya, tun daga kasashen Turai da Asiya da yankin gabas ta tsakiya da kuma nahiyar Afurka da sauran gurare.

Kanfanin diilancin labarai na Ahlulbayt din yaci gaba da cewa “Ya zuwa yanzu kusan kowacce rana muna yin zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, kuma wannan zanga zanga ta faro ne tun kusan farkon wannan shekarar, tun lokacin da muka fahimci halin rashin lafiya da Malaminmu yake fama da ita”

“Mun samu labarin mawuyacin halin da ya shiga na shanyewar barin jiki a inda ake tsare da shi, bayan kuma raunukan da yayi jinyarsu,wanda sojoji suka ji masa lokacin da suka kama shi, a kalla watanni 28 kenan”

“Muna bakin cikin gami da labarin da muka samu cewar Malaminmu ya rasa ido daya, tare kuma da fargabar rasa daya idon nasa idan har ba’a dauki matakan gaggawa ba na kare lafiyarsa”

“Yanzu kusan fiye da shekara guda kenan, babbar kotun daukaka kara ta tarayyar Najeriya, ta bayar da umarnin cewar cigaba da tsare Malam ya sabawa tanade tanade na kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma shiga hakkinsa ne a matsayinsa na dan kasa, dan haka ta bayar da umarnin a sake shi”

“Amma kuma, azzalumar Gwamnati Shugaba Buhari ta yi kunnen uwar shegu, ta cigaba da tsare shi ba tare da an caje shi ba, kuma aka hana masa samun kulawa ta lafiyarsa, wasu ‘yan kalilan ne kadai daga cikin iyalansa ake baiwa damar ganinsa”

“Zaman dirshan din da ‘yan uwa mabiya addinin Shi’ah suke yi da sauran ‘yan kungiyoyin kare hakkin bil adama na Najeriya suke yi dan ganin an sako Malam a wani kamfe na “Free Zakzaky” da ake yi, duk da cewar muna samun adadin masu fitowa wannan zanga zanga a kullum, amma dai ba haka muka so ba” A cewar kamfanin dillan labarai na AhlulBayt.

You may also like