Ɗan bindiga ya harbe ɗalibai da malamai a wata makaranta a Amurka



.

Wani mahari ya buɗe wa mutum shida wuta – waɗanda suka haɗa da yara uku da malamai uku a birnin Nashville na ƙasar Amurka.

Uku daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su ba su haura shekara tara ba da ke karatu a wata makaranta ta ƴan addinin kirista.

Ƴan sanda sun bayyana sunayen yaran da Evelyn Dieckhaus da Hallie Scruggs da William Kinney.

Sauran malaman da suka mutu sun haɗa da Cynthia Peak, mai shekara 61 da Katherine Koonce, mai shekara 60, da kuma Mike Hill, mai shekara 61.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like