- Marubuci, Alfred Lasteck, Munira Hussein da Anne Soy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga Dar es Salaam, Nairobi

Asalin hoton, NEMES TARIMO/FACEBOOK
Nemes Tarimo
Iyalin Nemes Tarimo, da ke Tanzania sun gargaɗe shi cewa kada ya amince ya shiga cikin sojojin Rasha domin yin yaƙi a Ukraine.
Sai dai ɗalibin mai shekara 33, ya amince da tayin da aka yi masa saboda zumar da aka lasa masa.
Yanzu mako uku ke nan bayan da iyalansa suka samu labarin rasuwar sa.
A gidan iyalansa, kowa na cikin jimami yayin da suke jiran ranar da gawarsa za ta iso gida Dar es Salaam.
Mutum 15 ne ke rayuwa a gidan iyalan Nemes da ke Dar es Salaam, ƴan uwa da abokan arziƙi na shigowa a kai-a kai domin jin ko akwai wani sabon bayani.
Ɗaya daga cikin ƴan uwansa ya ce lokaci na ƙarshe da suka yi magana da shi, shi ne a watan Oktoba, lokacin da ya shaida masu cewar ya amince zai shiga cikin dakarun sojin haya na Wagner na ƙasar Rasha domin fafatawa a fagen daga.
Ɗan uwan nasa, wanda bai son a bayyana sunansa ya ce “Nemes ya shaida min da wasu a cikin iyali cewa zai shiga dakarun Wagner, mun ba shi shawarar kada ya shiga.”
To sai dai an yi wa matashin, wanda iyalansa suka bayyana a matsayin mai haba-haba, kuma mai son taimako, tayin da ba zai iya cewa a’a ba.
Iyalan nasa sun ce ɗan nasu, wanda ke da burin zama ɗan majalisa ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta Chadema, ya je birnin Moscow ne domin yin karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar sadarwar zamani, a jami’ar Russian Technological University.
Sai dai an yanke masa hukuncin ɗauri bayan zargin sa da hannu a wasu laifukan da suka shafi ta’ammuli da ƙwaya.
A bara sai aka ce masa za a sake shi idan ya yi wa Rasha yaƙi, idan kuma ba haka ba, to zai ci gaba da zama a ɗaure.
Daga nan sai ya ce zai fafata domin ƴanta kansa.
Ƴan uwan Tarimo biyu: Roida Sambulika (hagu) da Rehema Kigobe
Wannan ya yi kama da labarin wani ɗalibi ɗan Zambia mai shekara 23, Lemekhani Nyirenda, wanda shi ma yake zaman gidan yari a Rasha, inda daga baya aka samu rahoton mutuwarsa a fagen daga.
Ministan harkokin waje na Zambia, Stanley Kakubo ya shaida wa majalisar cewa an faɗa masa yadda ake yi wa fursunoni alƙawarin yafiya idan suka amince suka shiga yaƙi tare da dakarun Rasha.
A watan Satumban da ya gabata an nuno shugaban sojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, a cikin wani bidiyo da ya yaɗu, ya na bayyana dokokin shiga yaƙi, ciki har da haramcin guduwa daga fagen fama, da haramcin saduwa da matan Ukraine, daga nan ya bai wa fursunoni minti biyar su yanke shawara kan ko za su shiga yaƙin ko kuma a’a.
Iyalan Nemes Tarimo sun gano cewa ɗan nasu ya rasa ransa ne a watan Oktoba, a Ukraine, lokacin da yake fafatawa tare da mayaƙan Wagner.
“Mun yi magana da shi ta ƙarshe ne a ranar 17 ga watan Oktoba, lokacin yana tare da dakarun Wagner. Daga nan sai muka samu labarin mutuwarsa a wurin abokansa na can a watan Disamba.”
Bayanai sun nuna cewa ya mutu ne sanadiyyar luguden wuta na dakarun Ukraine.
Kamfanin dillancin labaru na Federal News Agency da ke Rasha ya wallafa wani bidiyo da ya bayyana a matsayin na zaman makokin Nemes Tarimo a wani coci da ke garin Goryachiy Klyuch.
Kafar ta ruwaito cewa ya mutu ne a ranar 24 ga watan Oktoba a kusa da Bakhmut, wurin da aka gwabza ƙazamin faɗa cikin watannin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaru na gwamnatin Rasha, Ria Novosti ya tattauna da wani mutum wanda ya ce tare suke da Tarimo a filin daga.
Ya ce ɗan Tanzania ɗin ya mutu ne a lokacin da yake ƙoƙarin taimaka wa wani soja da aka raunata.
Kamfanin dillancin labarun ya ce kamfanin Wagner ya bai wa mamacin lambar girmamawa ta jarumta bayan mutuwar tasa.
Iyalan Tarimo na ci gaba da tattaunawa da ofishin jakadancin Tanzania a Rasha, sai dai har yanzu hukumomin na Tanzania ba su ce uffan ba kan mutuwar ɗalibin.
Iyalan Tarimo na son sun bizine shi a ƙauyensu da ke yankin kudancin Tanzania, to sai dai har yanzu suna nan suna dakon gawar ɗan nasu.
Ɗaya daga cikin ƴan uwansa ya ce “har yanzu ba mu gama yarda cewa ya mutu ba har sai mun ga gawarsa.”
Ƴar uwar mahaifinsa, Roida Sambulika ta ce “mun yi baƙin cikin rashin ɗanmu. Har yanzu ba mu san ranar da gawarsa za ta iso ba, amma tun mako ɗaya da ya gabata mun shirya tsaf domin yi masa sutura ta mutunci.”