​Amurka: An kama wanda ake zargin ya kashe Limami Da mataimakinsa


Rundunar ‘yan sandan birnin New York na Amirka, ta kama wani mutun da ake zargi da kisan Limamin wani masallaci da mataimakinsa a gundumar Queens.Gawarwakin Limam Maulama Akonjee da maitaimakinsa Thara Uddin.

Mutumin da aka kama mai suna Oscar Morel mazaunin Brooklyn mai shekaru 35 da haihuwa, an kama shi da laifin kisan kai, tare da mallakar makami a cewar babban sifeton ‘yan sandan birnin New York Hubert Reyes. A shejaranjiya Litinin ne dai aka gudanar da addu’o’i ga marigayi Imam Maulama Akonjee mai shekaru 55 da haihuwa da mataimakinsa Thara Uddin mai shekaru 64 da haifuwa, inda daruruwan mutane suka hallara a Brooklyn.

Musulman dai na birnin New York sun yi kira ga hukumomi da su dauki kwararan matakai domin basu kariya, tare da fatan ganin an hukunta duk wani mai hannu cikin wannan lamari.

You may also like