​Ernest Nolte masanin tarihin Jamus ya rasu


Allah ya yi wa shahararan masanin tarihin nan na Jamus, Ernst Nolte rasuwa a Berlin.Nolte wanda ke daya daga cikin masanan tarihin kasar ta Jamus wanda ya yi suna sossai ya kasance mafi yin kwankwanto, kana mafi haddasa sabannin ra’ayoyi a tsakanin akidoji a cikin rubuce-rubucen da ya rika yi.
A shekara ta 1980 ya rubuta wani littafi mai suna abin da ya wuce wanda kuma bai son ya wuce,Wanda ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin masana tarihin kasar da aka kira yakin masana. A cikin litafin da ya wallafa Nolte ya nuna banbanci da ke tsakanin akidar Nazis da Communist. Nolte wanda aka haifa a Witten a yammacin Jamus ya rasu yana da shekaru 93.

You may also like