​Najeriya: Yunkurin samar da wutar lantarki ta ruwa


Jihohin arewacin Najeriya shida suna matsa lamba a bisa neman tabbatar da hukumar HYPPERDEC da gwamnatin kasar ta kai ga kafawa can baya.
Sama da shekaru shida an gaza samar da hukumar sauya rayuwar al’ummar da suke samar da wutar lantarki ta ruwa a cikin tarrayar Najeriya, to sai dai a yanzu jihohin arewacin kasar na sabon yunkuri na ganin an tabatar da kafa hukumar HYPPERDEC don cimma gajiyar wuta a jihohinsu.

Jihohin dai sun gana a Abuja da nufin tabbatar daalkawarin kafa hukumar da za ta samar da kaso akalla 30 cikin 100 na wutar da aka samo a jihohin domin amfanin al’umma. 

A jihar Neja kadai dai alal misali sama da Megawatt 1000 ko kuma kaso 20 cikin 100 na daukacin wutar kasar ne dai madatsu guda hudu na Shiroro da Jebba da Kainji da kuma Zungeru ke samar wa ya zuwa yanzu, amma kuma ba tare da kaiwa ga cin moriyar wutar a tsakanin al’ummar jihar ba. 

Abubakar Sani Bello shin ne gwamnan jihar Nejam, ya ce:”Tilas a sauya akalar tafiyar da dukkanin lamura,an karbe gidaje da gonakin al’umma a lokacin da ake samar da shirin madatsun ruwan.”Fatan jihohin dai na kan gwamnatin Shugaba Buhari wajen share musu hawaye. 

Ko bayan Neja dai ‘ya’yan jihar Kebbi ma dai sun ce samma kal game da batun wutar da ya zuwa yanzu ke sanadiyyar lalata gonaki da karin fatara ba tare da basu dama ta cin gajiyar ta ba. 

Babale Umar Yawuri shi ne sakataren gwamnatin jihar Kebbi da ke cewa:”Mutanen Yawuri sun dau tsawon lokaci ba tare da samun wutar lantarki ba, kafa wannan hukuma zai taimaka wajen rage yawan matsalolinda al’umma ke fama da su.”A cikin watan Augustan shekara ta 2010 ne dai majalisun tarrayar Najeriya suka amince da kafa dokar samar da hukumar da aka dorawa alhakin samar da aiyukan raya kasa da ma kula da lafiya da muhallin al’ummar da harkar samar da wutar ta shafa. To sai dai kuma har ya zuwa yanzu siyasar kudu da arewacin kasar ta gaza kyalewa a kai ga tabbatar da hukumar da aka tsara hedikwatar ta a jihar Neja.

You may also like