Rundunar Sojan Ruwa ta Nijeriya ta Kera kananan jiragen ruwa wadanda za a yi amfani da su wajen fatattaka mayakan tsagerun Niger Delta.
Da yake kaddamar da jiragen, Karamin Ministan Tsaro, Mohammed Dan Ali ya nuna cewa ba ya ga jiragen yakin ruwan, haka ma, sojojin sun kera motocin sintiri wadanda za a yi amfani da su wajen fatattakan masu fasa bututun mai.
Ya kara da cewa an sanya wa jiragen yakin ruwa makaman da suka dace da kuma na’urar da za ta ba su kariya daga harin makami mai linzami inda ya yaba wa Shugaba Buhari bisa hadin kai da ya bayar wajen samun nasarar kera jiragen duk da rashin kudi da kasar ke fuskanta.