′Yan ta′adda sun kashe mutane Kwango | Labarai | DWShugaban kungiyar matasan yankin Anayey Bandigama ya ce mayakan kungiyar ADF ne suka kai hari na kauyen Kyamata da ke lardin Ituri. Hukumomi sun kuma sanar da cewa tuni aka birnin wadanda suka gamu da ajalinsa a kabari guda daya.

A cikin sanarwar da masarautar kauyen ta fitar, ta ce harin ya razana mazauna kauyen, inda a yanzu kimanin kashi 70 cikin dari na al’ummar yanki ne suke gudun hijira. Kasar Kwango dai ta shafe gomman shekaru ta na fama da ringingimu na tsaro da suka yi sanadiyar rayukan jama’a da dama.

 You may also like