A Shirye Gwamnatin Jihar Gombe Take, Da Ta Aiwatar Da Mafi Ƙarancin Albashi Na Naira 56,000


Ibrahim-Dankwambo

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya tabbatarwa da ma’aikatan jihar cewa a shirye gwamnatinsa take, ta aiwatar da mafi ƙarancin albashi na naira 56,000 ,matuƙar gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Dankwambo ya bada wannan tabbacin ne a ranar litinin, a wurin bikin tunawa da ranar ma’aikata ta shekarar 2017 da aka gudanar a Gombe.

Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Mista Charles Iliya wanda har ila yau  shine muƙaddashin gwamnan jihar.

“Da zarar gwamnatin tarayya ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi, gwamnatin mu zata aiwatar dashi dai -dai ƙarfin tattalin arzikin mu”yace

Yayi kira da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da su kasance masu juriya da kuma taimakawa gwamnati a ƙoƙarin da take na fitar da ƙasarnan daga matsalar tattalin arziki da take fama dashi.

Tun farko a nasa jawabin shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC reshen jihar, Aliyu Kamara yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da mafi ƙarancin albashi, dake ƙunshe a rahoton da kwamitin ƙwararru ya miƙa mata.

Amincewa da mafi ƙarancin albashin ya zama wajibi duba da matsin tattalin arzikin da ake fama dashi da kuma yadda kayan amfanin yau da kullum suka yi tsada.

 

 

 

You may also like