Shugaba Barack Obama da tsohuwar abokiyar hamayyarsa , wato Hillary Clinton da yanzu take neman ta gajeshi, sun hada karfi da karfe sun kaddamar da kemfen tare a jihar North Carolina.
Shugaban yace “na tsuma kuma Hillary ta tsumani saboda haka ashirye nake na yi aiki tukuru” inji Obama yayinda yake yiwa dimbin magoya bayansu jawabi a gangamin da suka yi a birnin Charlotte dake jihar North Carolina jiya Talata.
Hillary Clinton da magoya bayanta
Obama ya gabatar da Hillary Clinton tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar a matsayin mace mai kwakwalwa, mai hazaka, wadda kuma ta fi kowa cancanta ta zama shugabar kasa. Yace Hillary shugaba ce mai zuciya da karfin hali amma kuma mai jin tausayi wadda zata kare kasar. Zata taimaki iyalai ta kuma kare muradun Amurka.
Shugaba Obama yace zata san yadda zata samu goyon bayan kasashen duniya akan muradunmu yaynda kuma zata tabbatar sauran kasashen su ma sun tashi tsaye sun yi abun da yakamata. Sai Obama yace “dalilan ke nan da suka sa ta cancanci ta zama shugabar kasar Amurka” injishi.
Har yanzu Shugaba Obama nada matukar farin jini kuma goyon bayan da ya ba Hillary Clinton zai taimaka matuka.