Magoya bayan Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje sun afkawa juna da sara gami da jifa a ofishin jam’iyyar APC da ke unguwar Hotoro a karamar hukumar Nassarawa.
Rikicin ya wanzu ne tsakanin kungiyoyin Taurari Uku (3 Star) da kuma Taurari Biyu (2 Star) wadanda duk ‘yan Gandujiyya ne da suka samu rabuwar kai a tsakanin su. Wani jigo a jam’iyyar ya shaidawa jaridar arewa cewa, an shirya taro ne tsakanin kungiyoyin biyu domin tarar dan takarar shugaban karamar hukumar Nassarawa Dakta Lamin Sani Kawaji gami da dinke rikicin da ke tsakanin su.
Jim kadan bayan fara taro sai wasu suka fara cire makami suna nuna adawa ga Dakta Lamin Sani, a yayin da aka fara rarrashin su sai suka fara ruwan duwatsu gami da sare-sare. A cewar sa wasu da dama sun samu raunuka, lamarin da ta kai ‘yansanda sun yi harbi domin kwantar da kurar.
Wannan turka-turka tsakanin kungiyoyin biyu ta kara zafafa ne a yayin da Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi amai ya lashe a lokacin da ya ayyana sunan Muhammad Garba Shehu daga tsagin 2 Star a matsayin dan takarar karamar hukumar Nassarawa. Kana kuma daga bisani ya janye gami da bayar da sunan Dakta Lamin wanda dan tsagin 3 Star ne.
Wakilin mu ya tuntubi kakakin rundunar yansandan jihar Kano DSP Musa Magaji Majiya, sai dai bai daga ba, amma daga bisani idan ya samu sukuni za a ji yadda ta kaya.