2019 shekarar  Atiku ce – Fatima Muhammad


Fatima Muhamma, shugabar wata kungiya ta magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ake kira Atikunation Independent Campaign Group (ICG) a turance ,tace shekarar 2019 ta Atiku ce.

A wata tattaunawa da  Global Excellence, shugabar tace burin kungiyar tasu shine su gabatarwa da yan Najeriya da cikakken halayen Atiku Abubakar da kuma yi masa yaƙin neman zabe.

 A cewar ta Abubakar shine dan takara da daya tilo da  zai iya fitar da kasarnan daga mawuyacin halin da take ciki.

Da aka tambayeta ko kungiyarta na da goyon bayan mataimakin shugaban kasar sai ta ce :” kawai zan ce kujira kuga yadda abubuwa za su kaya nan ba dadewa ba, zaku samu amsar wannan tambaya daga bakin mai girma Alhaji Atiku Abubakar da kansa.

“Lallai shekarar 2019 ta Atiku ce domin alamu ƙarara sun nuna hakan.” 

Muhammad ta kara da cewa Atiku yayi dai-dai da ya fice daga jam’iyar APC.

Takara da cewa za ta shawarce shi ya dawo jam’iyar PDP duk da rikicin da jam’iyar ke fama da shi.

You may also like