2019 Shugaba Buhari Zai Kasance Shi Kadai a Jam’iyyar APC – Buba Galadima


Alhaji Buba Galadima, daya daga cikin makusantan Janar Muhammadu Buhari da suka yi gwagwarmayar siyasa a 2003, 2007, 2011 da kuma 2015 ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta zama kamar Marainiya, saboda ta gaza samun wanda zai dauki alhakin warware matsalolin rikicin cikin gida da ya yi wa Jam’iyyar katutu. 
Buba Galadima ya bayyana halin ko in kula na Buhari dangane da rikicin Jam’iyyar zai iya haifar da rushewar ta.

Wanda a karshe hakan zai bar Buhari ba tsuntsu ba kuma tarko yayin da ya yi kwadayin kara tsayawa takara a 2019 bisa doron Jam’iyyar. Domin za ta koma tamkar kangon da ba kowa a ciki.

You may also like